Thursday 6 November 2014

Ilimi gishirin zaman duniya.

 Ilimi gishirin zaman duniya. Idan babu ilimi, babu rayuwa mai kyau. Kamar ayyad aka sani a addinin Musulunci, ilimi wajibi ne ga kuwan Namiji ko Mace. Mace kamar Namiji, akwai bukatar tayi ilimi domin kuwa, ita uwa ce, ita ke renun ya'ya, kuma halayan ta da dabi'un ta abun kwaykwayo ne ga ya'yan ta.
    A can da lokutan da suka wuce, Mace ba'a ba su daman neman ilimi sosai ba. Hasalima dai, ilimi ko na Muhammadiya ko na zamani akan ce banasu bane. Har ana cewa "Sabbi saukar Mata". Watau da sun kai Suratul Sabbi shi ke nan sun bar karatu da neman ilimi. Suratul Sabbi kuwa itace Surah ta chis'in da bakwai a Alkur 'ani, kuma ita ce Izifi na Daya daga cikin Izfi Shttin dake a Alkur'ani. Mace a waccan zamanin , da ta kai shekara Sha Hudu ko Sha Biyar sai ayi mata aure. Hakan yana da kyau kamar yadda addinin ya nuna. Yin aure bai kamata ya zamu hani ga Ilimin ya' Mace ba. Sai a barsu gida basu san ko tsarki ba.
   Daga baya da Ilimin Boko za fara shigowa kashashen Hausa, an dauki karatun Boko a matsayin wani abu ba marar anfani. Duka ya'ya Maza da Mata ba'a basu dama suyi karatun ba. Daga baya bayan an samu yancin kai, sai aka fara ganin amfanin abu, toh fa lokacin ne aka fara bawa ya'ya Maza dama sosai sunayin karatun.
   A manyan makarantun Boko, akwai sashuka daban daban wadanda dalibi zai iya yin karatu. Akwai kamar Likitanci, karatun zama Injiniya, karatun harshuka irinsu Turanci D.s.s. A karatun Likitanci da Unguwar Zoma, wadannan sashuka ne wadanda mata zasuyi kuma ya amfani al'ummah. A wasu asibitocin, Maza ne wadanda ba Muharramai ba ke duba Mata. Toh a miyakon haka, zaifi kyau ace Mace yar'uwa irin ta ke duba ta.
  Mafi yawancin tsokacin mutane akan karatun ya'ya Mata akan yanayin makarantun ne. Yadda ake hada Maza da Maza, yadda tsarin sanya tufafi yake D.s.s. Idan dai har Gwamnati naso ta habbaka ilimin Mata a Nigeria, musamman a Arewacin Najeriya, ya zama dole ga Gwamnati tayi la'akari da halayya, addini, zamantakewa da kuma al'adun mutune wajen tsara makarantu da kuma yadda ake karatun, haka zai taimaka sosai wajen habba ilimi sosai a Arewacin Najeriya.

Comrade Abdulbaqi Aliyu Jari
Jami'ar Usmanu Danfoyo
+2348035424321
Sent from my BlackBerry wireless device from MTN

No comments:

Post a Comment