Sunday 2 November 2014

IHAME: yun kurin samar da haruffa da hanyar sadarwa ta hausa

 Farko dai, sunana Abdulbaqi Aliyu Jari. Ni dalibi ne a jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato. Ni dalibin tsangayar kimiyya ne,
sashen nazarin halittu (biochemistry).
  Akwai wani yunkuri wanda nike yi domin kirkiro da haruffa da alamomi rubutu na Hausa. Domin kuwa, hausa bata da wasu haruffa ko alamomi na rubutu nata na kanta. Ana dai amfani ne da la'alla na larabci, watau Ajami ko kuma na turanci watau na boko.
  To su wadannan hanya na larabci da Turanci wadanda muke amfani dasu suna
da nakasu. Asali dai shi ajami shine ya fara shigowa kasar hausa tun lokacin shigowar addinin musulunci. Wanda daga baya ne wali
dan masani ya gyar shi aka samu su k mai lankwas d.s.s. Shi dai ajami har wayau babu wata takamammiyar hanyr rubuta shi, hasali mane yasa aka yi mashi suna da "Ajami
gagari mai shi" domin yanzu kana iya ruburawa, zuwa anjima ka manta abund
ka rubuta da hannunka.
   Shi ma na turawa bayan shigowarshi a karni na ashirin bayan faduwr daular Usmaniyya a alif Dari Tara da Ukku, yashigo
kuma ya samu karbuwa sosai,wanda daga baya  shima aka gyara shi aka samu su k mai lan kwasa d.s.s
   Shi dai wanna  aiki nawa na fara shi kamar shekara daya da ta wuce. A lokacin da na fara wannan aiki, naje na samu Farfesa Abdullahi Birniwa na Jaminar Usmanu Danfodiyo, inda ya fara duba aikin yana bada shawarwari. Daga bisani kuma, sai naje na samu farfeas Aliyu Muhammad Bunza, tsohon shugaban tsangaya na art d kuma musulunci, inda yayi farinciki sosai kuma
yasha alwashin taimakama wannan aiki. Daga bisani kuma, ya tura ni wajen Farfesa Salisu Ahmad Yakasai, shugaban fannin
hausa na Jaminar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato, aiki sai maishi, nan da nan muka
fara aiki gadan-gadan da farfesa.
   Allah da ikon shi, daga lijacin zuwa yanzu mun samu nasara sosai akan wannan aiki. Domin kuwa, mun samu gabatarda makala a nan jami'a, sannan mun samu yin hira da gidajen Radiyo na fm da kuma rediyon jiha takatsina. sannan kuma a gidajen talabijin na NTA Katsina da Sakkwato. da kum talabijin ta jiha ta katsina. an kuma kaishi wajaje da yawa kamar su mariganyi wakilin tarihi na Daura, Fadar Sarakunan Katsina da Daura, nat libarary, education resources
centres.
   Har wayau kum, munyi kokarin hada gyiwa da cibiyar nazarin Hausa dake Sakkwato, kano da zaria. sannan akwai wata Journal ta sashen hausa wanda aka sa wannan rubutu
nawa.d.s.s.
  Fatan da nikeyi anan shine, BBC Hausa gidan rediyo ne mai albarka kuma mai sunan gaske, da su bani dama muyi hira, inda zan sake samun dama domin in yiwa al'ummar Hausawa albishir din cewa, harshe Hausa na
nan na samun cigaba da daukak. kuma yana nan a matsayin shi na harsge mafi daukaka
afirika. kula akwai sama da mutum Milliyan Dari Biyar dale iya sadarwa da shi. nagode kwari voa hausa na iya tun tuba ta a wannan email din nawa, ko a facebook a Abdulbaqi Jari ko
  kuma a wannan lambar wayar: 08035424321.


No comments:

Post a Comment