Dan Allah a bani dama in mika sakona na taya murna ga talakan Najeriya da kuma ga Janar Muhammadu Buhari murnar lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar shi ta APC da akayi ranar 11 ga Watan Disamba 2014. Ko shakka babu zaben Janar Buhari da akayi, anyi shi ne akan cancanta da kuma kyautata tsammani da Jama'a suke yi mashi akan zai kamanta adalci, gaskiya da kuma tsoron Allah akan shugabancin Kasar Najeriya idan Allah ya bashi dama. Ina kara taya talakan Najeriya murnar tsaida Janar Buhari da sukayi.
Ba ma wannan kadai ba, Janar Buhari yayi rawar gani a wasu mukamai daya taba rikewa a can baya kamar su; asusun albar katun man fetir (PTF), Ministan man Fetir D.S.S. Janar Buhari yayi kokari sosai domin kamanta gaskiya da rigon amanar jama'a da adalci da gaskiya, wanda hakan ne ma yasa jama'a ke ta fata, da kuma kokarin ganin cewa ya dawo, la'alla ko an samu sawaba akan yanayin da ake fama da shi na; Talauci, rashin tsaro, rashawa, da kuma cin hanci.
Mutane dole suje su anshi katin zabe, kuma su fita suyi zabe, idan an gama zaben kuma, a kasa a tsare, a raka kuri'un kuma kamar yadda akayi a 2011. Dole kowa yayi bakin kokarin shi domin aga an samu chanjin da ake bukata.
Ina kira ga Jama'ar Najeriya da kuma Janar Buhari da su kara sanya Allah Mataukaki a matsayin jagoranshi, ya kuma zabi mataimaki mai halin na gari irin nashi koda musulmi ne kuma, kada ace wai dole sai wanda ba musulmi ba.
Ubangiji Allah ya shige mana gaba, Allah ya bamu lafiya da zama lafiya. Allah kuma ya zaba mana shuwagabanni masu tsoron shi, kuma masu adalci.

No comments:
Post a Comment